Home

Music

Video

Kanny

Tags:

SOYAYYAR JARUMI RAM CHARAN DA MATARSA

 A yau zamu leka kasar Indiya ne domin zakulo muku wani dan taba ka lashe daga masana'antar Fim ta Bollywood,


Zamuyi magana ne game da yadda akayi madoya 2 suka hadu harta kaisu ga aure,


Jarumin kudancin Indiya Ram Charan da matarsa Upsi.


Jarumi Ram Charan sun fara haduwa da matar sa Upsi ne a wani Club dake a birnin London na kasar burtaniya basuyi wata wata ba wajen kulla abota wanda daga bisani abotar ta sauya zuwa soyayya a karshe dai har suka aminta zasu auri juna,


Madam Upsi ta kasance mace mai tsananin kaunar mijinta wanda hakan yasa take matukar kishin sa kuma ko kadan bata son yayi nesa da ita hakan ne ma yasa a mafi yawan lokuta takan kai masa ziyara a wuraren da yake aikinsa na Fim,

Sai dai wani abu days rika ciwa Upsi tuwo a kwarya shine yadda masoyan mijin nata suke ganin matar bata dace dashi ba kasancewar tana da girman jiki wanda hakan yasa tabi hanyoyin motsa jiki da sauransu wajen daidaita tsarin jikin ta domin samun dacewa da masoyin nata kamar yadda masoya suka bukata,

Acikin Shekara ta 2016 akai ta yaɗa jita-jitar cewa Charan yasaki matarsa, inda hakan yazamo topic mafi tattaunawa a shafukan sada zumunta na zamani, amma ita tayi alawadai da wannan batu da masu yadashi,


Inda ta mayar da martani da cewa ita da mijinta ƙaunace mai ƙarfi kuma sai abinda yaci gaba,"


Tana da Dukiyar gaske kuma ta samu shaidar kammala karatunta na Degree akan International Business Marketing & Management daga wata jami'a da ke ƙasar London,

Upasana da jaruma Tamanna sun kasance Aminan juna don saboda ƙwazon da ta nuna acikin shirin Sirikinta Syee Raa Narisimha Reddy acikin shekara ta 2019, upasana don jin daɗin hakan tayiwa jaruma Tamanna Kyautar ƙaton Zobe na Lu'uLu da yaƙutu.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Privacy Policy | About Us | Contact | Terms and condition
KOYARWA DA NISHADANTARWA SUNE ALKIBLAR MU | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Abdulmusa