Home

Music

Video

Kanny

Tags:

SHEKARU 23 DA FITAR FIM DIN PARDES KASUWA

A ranar 8 ga wannan wata na August shekarar 2020 da muke ciki ne Fim din PARDES ya cika shekaru 23 cif domin kuwa ansaki Fim din ne a ranar 8 ga watan August 1997,

Abun da Fim din ya kunsa a takaice.


Film din PARDES yana bada labarin Arjun da Ganga. yana nuni ne game da yadda kyawawan ɗabi'u da al'adu na Indiyawa suka ci nasara akan na turawan yamma.

Akwai wani hamshaƙin attajiri mai suna Kishorilal wanda yake zaune a Amurka yana gudanar da kasuwancinsa a can sai ya kawo ziyara ƙasar sa ta haihuwa wato kasar Indiya wajen abokinsa mai suna Suraj Dev, anan ne yaga yadda suke riƙo da al'adu da ɗabi'u na Indiya sai abin ya burge shi har yaga wata yarinya mai suna Ganga wacce take babbar 'ya ce ga abokin nasa,

Kishorilal baiyi wata wata ba ya nemi a haɗa aure tsakanin ita Ganga ɗin da kuma ɗansa mai suna Rajiv wanda shi kuma ya kasance a can Turai ɗin yake ya manta da duk wasu ɗabi'u na Indiya. bayan ya koma can Amurka ne ya turo wani saurayi mai suna Arjun wanda ya kasance ɗan riƙo ga shi Kishorilal ɗin domin yayi ja gaba wajen gudanar da shirye shiryen bikin.


Ko kunsan meya faru?


Wannan duk yana cikin  shirin PARDES.

Mashiryin shirin Subash Ghai ne ya shirya ya kuma bayar da umarni

'Yan wasa sun hada da Shah Rukh Khan, Mahima Chaudhry, Amrish Puri,
Apurva Agnihotri da Alok Nath ne suka jagoranci shirin.

Shirin yana kunshe da wakoki masu dadin gaske kamar
1. Nahin Hona Tha
2. Meri Mehbooba
3. Yeh Dil Deewana
4. I love My India
5. My First Day In USA
6. Do Dil Mil Rahe Hain
7. Jahan Piya Wahan Main

Tsawon Fim din shine mintuna 191

Share this


0 comments:

Post a Comment

Privacy Policy | About Us | Contact | Terms and condition
KOYARWA DA NISHADANTARWA SUNE ALKIBLAR MU | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Abdulmusa