Home

Music

Video

Kanny

Tags:

JARUMAN BOLLYWOOD DA BASA GA MACIJI DA JUNA

A yau zamu leka masana'antar Fim ta Bollywood dake a kasar Indiya domin zakulo muku yadda rashin jutuwa take shiga tsakanin manyan jarumai mata,

Kamar dai yadda kowa ya sani akan samu rashin jituwa tsakanin mutane sabo da wani dalili.

Suma jarukan Fim na Bollywood ba'a barsu a baya ba domin kuwa... Kubiyoni

Gadai jerangiyar wadansu jaruman masana'antar da basa ga maciji da juna

1. Anusha Sharma. da Depeeka Padkune.

Dalilin samun sabaninsu shine jarumi Ranveer Singh yana soyayya da Anushka kai tsaye yayi tsalle ya koma soyayya da abokiyar sana'arta wato Deepika wanda hakan ya haifar da rashin jituwa a tsakanin jarukan biyu,

2. Bipasha Basu. da Kareena Kapoor.

Dalilin samun sabani a tsakaninsu ya samo asali ne tun a Fim din Ajnabee wani rikici ya hadasu wanda hakan yasa basu sake haduwa a Fim ba.

3. Katrina Kaif. da Deepika Padukone.

Ranbir Kapoor ya fara soyayya da Deepika karshe ya koma ga Katrika wannan ne dalilin samun sabani tsakanin jarukan.


4. Karena Kapoor. da Priyanka Chopra.

Rashin jituwarsu saboda Shahid Kapoor yayi soyayya da kareena daga baya yakoma ga Priyanka sannan bayan haka kasancewar dukaninsu jaruman sunfito a fim daya me suna Aitrazz Priyanka tafi samun yabo acikin fim din fiye da kareena wanda hakan bai yiwa Kareena dadiba wannan dalili ne yasa basa shiri da juna.

5. Katrina kaif. da Alia Bhatt.

Alia Bhat da Katrina Kaif sun kasance aminan juna Ranveer Kapoor yana soyayya da ita Katrina sai kawai aka wayi gari ya juyar da Soyayyarsa zuwa ga Alia Bhat wanda hakan shine silar bullar rashin jituwa tsakanin jaruman.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Privacy Policy | About Us | Contact | Terms and condition
KOYARWA DA NISHADANTARWA SUNE ALKIBLAR MU | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Abdulmusa