Home

Music

Video

Kanny

Tags:

GWAMNATI ZATA RABAWA MATASA JARI DOMIN DOGARO DA KAI

Gwamnatin tarayya ta fitar da zunzurutun kudi har Naira Biliyan 75 domin bayar da bashin dogaro da kai ga matasa musamman masu kananan sana'o'i,

A lokacin da yake jawabi ga manema labarai a fadar shugaban kasa ranar laraba data gabata ministan matasa da wasanni Mr. Sunday Dare ya sanar da fara wannan kuduri nan bada dadewa ba,


Yace: akan haka aka kirkiri bankin matasa wanda zai rika wayar da kan matasan wannan kasa miliyan 68 masu shekaru daga 18 zuwa 35 akan harkar kasuwanci”,


Ya kuma shawarci matasan da suke da tunanin fara wani kasuwanci da su tuntubi kananan bankuna da ke bayar da bashi guda 125 a fadin kasar nan don karbar jari ga wadanda suka cancanta.

Dare ya bayar da tabbacin cewa za a yi adalci ga matasan wajen gudanar da shirin da za a aiwatar ta fasahar intanet.

Idan dai ba'a manta ba ko a baya bayan nan gwamnatin tarayya ta bayar da bashin Covid19 loan ga dubunnan mutane a kasarnan.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Privacy Policy | About Us | Contact | Terms and condition
KOYARWA DA NISHADANTARWA SUNE ALKIBLAR MU | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Abdulmusa