Home

Music

Video

Kanny

Tags:

ZAIRA WASIM TA GOGE ACCOUNT DIN TA NA TWITTER

Zaira Wasim ta fara samun dunbun magoya baya ne tun lokacin da ta fito a Fim din DANGAL tare da jarumi Ameer Khan, dan haka zamu iya cewa Zaira ta shigo Bollywood da kafar dama ganin yadda ta samu masoya a dan kankanin lokaci har zuwa lokacin da ta sanar da ficewar ta daga jarkar Fim sabo da tsare mutuncin ta da Addinin ta kamar yadda tayi bayani a lokacin,

Zaira Wasim wacce ta kasance yarinya ce Musulma ta fara fuskantar kalu bale a kasar India bayan da ta sanar da wucewar ta a harkar Fim sabo da tsare hakkin Adddinin ta,

A kwanakin nan da suka gabata ne wannan baiwar Allah tayi post da Ayar Al'qurani a shafin ta na Twitter wanda hakan ya jawo mata zagi da bakaken maganganu daga 'yan iska cikin masu bin Addinin Hindu wanda hakan ya kai ga Zaira ta goge Account din ta na Twitter da Instagram gabaki daya.

Allah mai taimakon bayin sa Jim kadan da faruwar haka sai ga wani Trending ya bayyana a Twitter mai taken #WeStandWithZairaWasim
Wanda masoya masu goyan bayanta musulmai da Wanda basu ba sukeyi Wanda hakan nasarace wajenta dan duk iskancin da akeyi a Bollywood dan samun soyayyar al'umma ne to itama barin da tayi yasa ma mutanen kirki sonta a ransu,

Mu fahimci ba kowane zai iya wan nan kokari na zaira ba na hakura da Daukaka, da kudin da ake samu a harkar da sauransu fatanmu Allah ya kara mata imani ya tsareta daga sharrin makiya.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Privacy Policy | About Us | Contact | Terms and condition
KOYARWA DA NISHADANTARWA SUNE ALKIBLAR MU | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Abdulmusa