Home

Music

Video

Kanny

Tags:

YADDA ZAKA DAKATAR DA MASU ADDING DIN KA A GROUPS


Yan uwa barkan mu da wannan lokaci. ba tare da bata lokaci ba a yau zanyi bayani ne game da yadda mutum zai dakatar da masu saka shi a Telegram Groups ba tare da sani ko amincewar sa ba,

Zan iya cewa kusan duk ma'abota kafar sadarwa na Telegram suna ko sun taba samun wannan matsala ta mutum ya wayi gari ya samu kansa a wani group da ba shi ya shiga ba kuma ba wani da ya sanar da shi zai saka shi a group din,

Wanda idan ba ayi sa'a ba ta dalilin hakan mutum zai iya fada wa hannun mazambata 'yan damfara duba da cewar a yanzu Telegram ya zama babbar tunga ga 'yan damfarar yanar gizo,


A wannan darasi zan koyar da yadda mutum zai dakatar da masu saka shi a Telegram groups ba tare da sanin sa ba,


Da farko dai ya kasance kana da Account a Telegram sai ka bude shi idan ka bude ka duba can saman wayar ka bangaren hannun hagu ka danna alamar Menu bayan ya bude zakaga jerangiyar rubutu sai ka taba Privacy and security zai bude maka shafi na gaba sai ka duba can kasa ka taba Groups bayan ya bude zaka samu alamar • tana a kan Everybody wato kowa ma zai iya add din ka a group koda kuwa a yau ya samu lambar ka,
To abun da zaka yi a nan shine sai ka mayar da shi kasa wato My Contact hakan yana nufin iya wadanda kake da lambarsu ne zasu iya add din ka a group kuma su din ma zaka iya zabar iya adadin mutanen da kake bukata su iya add din ka a group a duk lokacin da suke bukata.


Zan dakata a nan sai kuma lokaci na gaba idan Allah ya nuna mana,


Kuci gaba da kasancewa da Hausatk

Kuyi share a social media domin amfanar 'yan uwa da abokai.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Privacy Policy | About Us | Contact | Terms and condition
KOYARWA DA NISHADANTARWA SUNE ALKIBLAR MU | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Abdulmusa