Home

Music

Video

Kanny

Tags:

SHAH RUKH KHAN SHINE JARUMIN DA YAFI SAMUN KUDI

A yau zan kawo dalilan da yasa jarumi Shah Rukh Khan yafi ko wane jarumin Fim samun kudi koda kuwa bai saki sabon Fim ba, sai ku biyoni.

Babban jarumin Fim din nan na Bollywood sarki Shah Rukh Khan shine jarumin Fim da yafi ko wanne samun kudi a harkar Fim koda kuwa bai saki wani sabon Fim ba, Wani zaiyi mamakin hakan amma akwai dalilin da yasa,

Shah Rukh Khan dai yana daya ko ince layin farko farko cikin manyan 'yan Fim na duniya kuma dan kasuwa ne
Ko Shakka Babu Yana Daga Cikin Mutanen Da A Duniyarnan Ke Samun Kudi Koda Kuwa Bacci Suke. Amma Dalilan Samun Kudin Nasa Sune Kamar Haka.

Kamar Yadda Ya Fada Zai Iya Rawa A Wajen Biki Domin Kudi Sabanin Sauran jarumai, Ya Kasance Yana Rawa A Wajen Biki Tun Wajen 1995 Bayan Fitowa A Film Din DDLJ Amma Daga Baya Kasancewarsa Babban jarumi Hakan Baisa Ya Daina Ba Kawai Dai Ya kara Kudin Da Yake Karba Wanda Sunkai Kimanin 4-8 Crores Wanda Yace Shi A Gurinsa Ba Abin Kunya Bane Kawai Wannan Duk A Cikin Kasuwanci Ne.


Yana Matuqar Son Shirya Finafinai Da Suka Kunshi Fasaha Irin SFX (Special Effect) Inda Anan Yafi Kashe Kudinsa Domin Bayan Rushewar Kamfanin Su Shida Aziz Mirza Da Juhi Chawla Hakan Ya Bashi Damar kirqirar Red Chillies A Shekarar 2002 Wanda Suke Da Studio Guda Video Effect (VFX) Hakan Ya Bashi Damar kirqirar VFX Na Kansa Wanda Ba Kowa Keda Wannan Damar Ba. A kiyasin Da Akai Yana Samun 500 Crore Ka Sama Da Haka A Shekara.
Mutum Ne Me Matuqar Son Harkar Wasanni Inda Yana Da Kaso 55% A Qungiyar Cricket Ta Kolkata Knight Riders (KKR) Wanda Wajen Talla Take Cazar 22 Cr. A Gaban Riga 10 Cr. A Baya.
Tallace Tallace Anan Yafi Samun Kudi Domin Sabanin Sauran Actors Kamar Aamir Khan Sai Sun Zabi Abinda Zasuyi Talla Amma Shi Tun Daga Abu Mai Tsada Kamar Kamfanin Agogo Na Tag Heuer Izuwa Mai Araha Kamar Manshafawa Kamar Denver.
Sannan Shine A Fuskar Abubuwa Kamar ,Big Basket,Dish TV,Byju's Da Sauransu Wasu Kamfanin Ma Yana Da Share Aciki. Sannan Yakanyiwa Wasu Video Inda Yana Karbar 3.5 Cr. Kullum Duk Bidiyo Daya.
Wannan Yasa Koda Baiyi Film Ba A Shekara Yana Da Hanyoyin Samun Kudi Da Dama.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Privacy Policy | About Us | Contact | Terms and condition
KOYARWA DA NISHADANTARWA SUNE ALKIBLAR MU | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Abdulmusa