Home

Music

Video

Kanny

Tags:

MAI KWAIKWAYON MAGANAR BUHARI MC TAGWAYE YA ANGWANCE

Shahararren dan wasan barkwancin nan mai kwaikwayon shugaban Nigeria Buhari wato Mr. Obinna Simon Simon wanda akafi sani da MC TAGWAYE ya angwance da masoyiyar sa 'ya ga Maryam Uwais mai baiwa Shuaba Buhari shawara game da kyautata rayuwar Al'uma,

Dan wasan barkwancin wanda ya kasance dan kabilar Igbo yayi wuf da masoyiyar sa HAUWA a ranar asabar 14 ga watan April kamar yadda ya sanar a shafin sa na Instagram, Munyi aure cikin farin ciki a yau godiya," a cewar 'MC TAGWAYE'


Ita ma uwar amarya wato Maryam Uwais, ta tabbatar da auren a shafinta ta Instagram inda ta wallafa hotunan daurin auren. Inda ta rubuta cewa

'Ya ta Hauwa, ta yi aure yau. Kuma na samu sabon ɗa, MC Tagwaye,"

Ta yi kira ga abokan arziki da sauran al'umma su yi wa sabbin ma'auratan addu'ar zaman lafiya da kariya daga Ubangiji.

MC Tagwaye ya shahara ne sakamakon kwaikwayon maganganun Shugaba Buhari, inda yake magana tamkar shugaban.

Ya taɓa haɗuwa da shugaban kasar, wanda ya shi kansa ya sha yin dariya idan ya saurari yadda MC Tagwaye yake kwaikwayon maganganunsa

MC Tagwaye dan asalin jihar Anambra ne da ke kudu maso gabashin Najeriya, kuma yana yin sana'ar gabatar da jawabai na barkwanci musamman a wuraren bukukuwa.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Privacy Policy | About Us | Contact | Terms and condition
KOYARWA DA NISHADANTARWA SUNE ALKIBLAR MU | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Abdulmusa