Home

Music

Video

Kanny

Tags:

AN TSINCI GAWAR JARUMIN BOLLYWOOD A GIDAN SA
Jami'an tsaron kasar Indiya sun sanar da samun gawar jarumin Bollywood mai suna Sushant Singh Rajput a gidan sa dake birnin Mumbai,A lokacin da suke bayyana lamarin 'yan dandar kasar Indiya sunce: suna kyautata zaton kashe kansa yayi ta hanyar rataya,
Sai dai sunce sun samu bayanin dake nuna jarumin mai shekara 34 yana da tsohuwar damuwa a zuciyar sa,
Ya fito a fina-finai kamar Kai Po Che and M.S Dhoni -- tarihin ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan kuriket a Indiya.
A kwanakin da suka gaba ne kuma aka isko gawar manajan jarumin Disha Salian a mace.
Abokan sana'arsa da kuma masoyansa da dama ne suka yi jimamin rashinsa a Twitter tare da yin ta'aziyya ga iyalinsa.

Share this


0 comments:

Post a Comment

Privacy Policy | About Us | Contact | Terms and condition
KOYARWA DA NISHADANTARWA SUNE ALKIBLAR MU | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Abdulmusa